Tsohuwar matar fitaccen tauraron Kannywood, Ahmad S. Nuhu, ta bayyana mawuyacin halin da ta fada a ciki bayan rasuwarsa.
Hafsat Shehu ta bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa a yayin da tauraron yake cika shekara 15 da rasuwa.
Tauraron ya rasu ne ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007 sakamakon hatsarin mota a garin Azare na jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ta ce ta fada cikin matukar bakin ciki yadda “idan na ga wasu mutane suna dariya nakan tambayi mahaifiyata cewa yaushe zan yi dariya’?
A cewarta Ahmad Nuhu mutum ne da yake ganin mutunci da darajar mata.
source